Koda yake an yi haka ne farmakin da aka kai wa sojojin kasar Amurka bai tsaya ba ko kadan.
A gaban tsanantaccen halin dake cikin kasar Iraq a yanzu, a ran l7 ga watan nan da muke ciki, Janar George W.Casey babban kwamanda na kasar Amurka ya yi na'am cewa, kowanen kokarin da hadaddiyar rundunar sojan dake hade da sojojin Amurka da na Iraq za su yi, a lokacin yin babban zabe, ba shakka, farmakin da za a tayar ba a iya hanawa ba.
Masana suna gani cewa, koda yake an kasance da babban hadarin da zai iya auku,amma ba za a iya jinkirtar da babban zaben nan ba,domin kasar Amurka ta yi matukar kokarin neman yin babban zabe cikin daidai lokaci, domin wannan babban zaben da za a yi cikin daidai lokaci ya ba da abin shaida ga karfin iyawar kasar Amurka wajen sarrafa da kasar Iraq da munufar da gwamnatin Amurka take tafiyar da ita tana da gaskiya ko ba haka ba. Ban da haka kuma,in gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraq ta jinkirtar da wannan babban zabe za ta iya gamu da kiyewa daga yawancin mutane na kasar Iraq, ta haka ne ba mai yiyuwa ba ne za a jinkirtar da wannan babban zabe a kasar Iraq.(Dije) 1 2
|