Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na duniya ina labari na yau: a ran 30 ga watan nan da muke ciki, za a yi babban zabe a kasar Iraq, wato tsawon lokacin da za a yi babban zabe bai kai mako biyu ba, amma har wa yau dai halin da ake ciki a kasar Iraq bai sami kyautatuwa ba tukuna, Wato kasar Amurka da gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraq sun yi jayayya mai tsanani tare da masu damara na kasar Iraq. A ran l7 ga watan nan da muke ciki, wani hargitsi mai karfin tuwo da ya auku ya yi sanadiyar mutuwa gomai da masu jin rauni da yawa.Har an sa kasar Iraq wadda ta sha masifar yake yake ta sake gamu da wahalar zubar da jini.
A ran l7 ga watan, sashen soja na kasar Amurka dake kasar Iraq ya bayyana cewa, a cikin sawo'I 24 da suka shige,a birnin Mosul dake arewancin kasar Iraq, sojojin kasar Amurka suka tayar da babban farmaki, inda suka kashe masu damara 7 da kama mutane l2 wadanda suka yi adawa da kasar Amurka. Yanzu, a wuraren dake kewayen birnin Mosul, sojojin Amurka da rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta kasar Iraq sun tattara sojojinsu fiye da dubu l2 don kiyaye babban zaben da za a yi. Ban da haka kuma lardin Nineveh dake kewayen birnin Mosul shi ne daya daga cikin larduna guda hudu masu tsanantaccen hali, sabo da an gamu da kurarin da dakaru masu yin adawa da kasar Amurka suka yi musu, gaba daya ne 'yan kwamitin kula da babban zabe na wannan lardi dukkansu sun yi murabus daga aikinsu. Ta haka ne har yanzu ba a fara yin rijista ga aikin zabe ba tukuna. A wuraren dake kusa da birnin Fallujah, inda musulmi na rukunin Sunni ke da yawa sosai, a cikin sawo'I guda 48 da suka shige, rundunar sojan kiyaye zaman lafiya ta kasar Iraq ta yi kame kame, a kalla dai mutane 35 sun mutu wadanda suka yi adawa da kasar Amurka, har an kama mutane 64. a wurin dake kudancin garin Baquba dake arewancin kasar Iraq, a ran l7 ga watan da safe, rundunar sojan kiyaye zaman lafiyar kasar Iraq ta kama mutane wajen 60 wadanda suka yi adawa da kasar Amurka. Hukumar da abin ya shafa ta kasar Amurka da ta Iraq ta bayyana cewa, tare da kusantowar lokacin yin babban zabe, cikin gama guiwa ne sojojin kasar Amurka da na kasar Iraq za su kara karfin yin kame kame a wuraren da rukunin Sunni suke zaune a cunkushe. Don yin matukar kokari ga kago wani kyakkyawan hali na yin babban zabe.
1 2
|