Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-11 18:26:30    
Kofin Hopman

cri

Harry Hopman ya dade yana alla-allar shirya gasar cin kofin wasan kwallon tenis ta tsakanin kungoyi daidai da gasar cin kofin Davis da na Fed. Daga karshe bisa kokari da dalibansa Paul McNamee da Charlie Fancutt suka yi ne, aka bude gasar cin kofin Hopman a ran 28 ga watan Disamba na shekarar 1988, akwai kungiyoyi 8 wadanda suka shiga cikin wannan gasar. Matarsa Lucy Hopman ta kan bayar da kofin Hopman ga zakaran gasar a ko wace shekara.

Bisa ci gaba da ake samu wajen yin gasar cin kofin Hopman, gwanayen duniya da yawa su kan shiga gasar nan. Tun da aka shirya irin wannan gasa ta farko, sai Steffi Graf, sarauniyar wasan kwallon tenis ta duniya ta shiga cikin gasar, ta haka ta sama wa gasar kwarjini. Ban da ita kuma akwai sauran manyan taurari kamar su Monica Seles da Jana Novotna da Martina Hingis da John McEnroe da Goran Ivanisevic wadanda su ma sun taba shiga cikiin irin wannan gasar. Banban da haka gwanaye 'yan wasan kwallon tenis na Amurka ba su mai da hankali ga irin wannan gasa ba, Pete Sampras da Andre Agassi da 'yan'uwa mata Williams biyu wadanda su ne zakaran duniya ba su taba shiga cikin gasar nan ba.

 

 


1  2  3