Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2005-01-11 18:26:30    
Kofin Hopman

cri
Ya zuwa yanzu dai, kofin Hopman bai yi suna sosai ba, idan an kwantanta shi da shahararren kofin Davis da na Fed. Gasar cin kofin Hopman ta duniya ta wasan kwallon tenis tsakanin kungiyoyin gaurayar maza da mata, kuma an sami wannan sunan kofi ne daga wani shahararen namijin duniya da ake kira Harry Hopman. Matsayin kofin nan ya tashi daidai da na kofin Sudiman na wasan badamindo.

Harry Hopman wani shahararren dan wasan kwallon tenis ne na kasar Australiya. Amma ya sami babban ci gaba ne bayan zamansa malamin koyarwa. Ya taba koyar da 'yan wasan kwallon tenis da yawa na nahiyar Austaraliya da su zama manyan taurarin duniya. Daga cikinsu akwai Rod Laver, babban tauraro dan wasan kwallon tenis wanda shi ne kadai ya taba zama zakaran gasar wasan kwallon tenis mai suna "Great Salm" da aka yi tsakanin mata har sau biyu da sauransu. A karkashin jagorancin Harry Hopman, da kyar a yi tsammani cewa, kungiyar Australiya ta sami kofin Davis har sau 15. Bayan da ya yi kaura zuwa kasar Amurka a shekarun 1970, ya horar da manyan taurari 'yan wasan kwallon tenis kamar su John McEnroe da Andres Gomez da sauransu.


1  2  3