Sa'an nan har yanzu ba a gama shirye shiryen zabe ba tukuna. Kafofin watsa labaru sun lura da cewa, ana yin yakin neman zabe ne ta wata hanyar musamman, wato babu muhawara da taruruka. Yanzu mutane da yawa na Iraq suna kukan cewa, ko kusa ba za su iya gane 'yan takara ba, saabo da haka ba su iya yin zabin gaskiya ba. Kuma har yanzu ba a tabbatar da wuraren jefa kuri'a ba tukuna domin ana damuwa da farmakin da za a kai musu, kuma a asirce ne a ke neman ma'aikatan aikin zabe dubu 250 domin ana damuwa cewa, idan an bayar da sunayen ma'aikatan zabe, to nan da nan za a kai musu farmaki.
Na uku, ana shakka ko babban zabe zai wakilci nufin jama'a. a ran 27 ga watan Disamba, Jam'iyyar Islam wato babbar jam'iyyar siyasa ta rukun Sunni ta janye jiki daga babban zabe, wannan dai babban naushi ne ga babban zaben kasar Iraq.
An bayyana cewa, ko da ya ke gwamnatin wucin gadi ta kasar Iraq da gwamnatin Bush na kasar Amurka duk suna son yin zaben Iraq a daidai lokaci tare da nasara. Amma babban zabe ba wata dabarar da za ta warware duk matsalolin da ke gaban kasar Iraq ba. Idan gwamnatin Bush ta yi biris da hakikanin halin da a ke ciki a kasar Iraq ba ta tsaya ta yi zabe bisa shiri, to, mai yiwuwa ne kasar Amurka za ta kife cikin halin kaka ni ka yi a kasar Iraq. (Dogonyaro) 1 2
|