Ko da ya ke ana kusanto lokacin babban zabe na Iraq wato ran 30 ga watan Janairu, amma ko kadan babu zaman lafiya a kasar Iraq. A ran 4 ga watan nan an kashe Ali Al Haidri, shugaban lardin Bagadaza. Wannan ya sa ba wanda ya san makomar babban zaben da za a yi.
Babban zabe kuwa wani babban al'amari ne a wajen sake raya siyasar kasar Iraq, amma har yanzu ba a sani ba ko za a yi babban zabe a daidai lokaci.
Da farko, da wuyar kyautata halin da a ke ciki a kasar Iraq. Yanzu ana ta nuna karfin tuwo a duk fadin kasar Iraq. Bisa rahotannin da aka samu an ce, yanzu dakaru masu yin adawa da Amurka sun kai dubu 200, wato sun fi sojojin Amurka da ke a Iraq yawa. Dakaru masu yin adawa da Amurka suna iya kashe duk ma'aikatan gwamnatin wucin gadin da su ke son kashewa, amma sojoji masu kiyaye zaman lafiya na kasar Iraq ba su da karfin kiyaye zaman lafiyar ma'aikatan gwamnati. Ban da haka kuma wasu dakaru masu yin adawa da Amurka sun bayar da sanarwa don yin kira ga jama'ar kasar Iraq kada su shiga babban zabe, kuma sun yi barazana cewa, za su kai farmaki ga masu jefa kuri'a da tashoshin jefa kuri'a. Ko sakataren harkokin waje Colin Powell na Amurka ma ya yi na'am cewa, da ya ke lokacin babban zabe yana zuwa, za a kara kai farmaki da fasa bomabomai a cikin kasar Iraq. Yanzu a kasar Iraq kowa da kowa yana jin tsoron farmakin da za a kai musu. Cikin halin haka, ko jama'a za su jefa kuri'a? ko za a amince da sakamakon zaben da za a yi?
1 2
|