Bikin sallar bazara wato bikin ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin

Daidai kamar yadda Hausawa ke daukar babbar salla da muhimmanci, Sinawa su kan dauki sallar bazara wato ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin da matukar muhimmanci a duk shekara. Ko da yake zamani na samun sauye-sauye, amma duk da haka Sinawa ba za su canja wannan al'adarsu ta gargajiya ba.

Ran 9 ga watan Febrairu ranar sabuwar shekarar nan ce bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin. An ce, yau da sama da shekaru 4,000 ke nan da Sinawa ke murnar sallar bazara, amma tun can farko, ba a kiran sallar nan sallar bazara, kuma ba a tsaida ranar da ake murnar sallar nan ba. Sai zuwa shekaru 2100 da ‘yan doriya kafin bayyanuwar Annabi Isa (A.S.), Sinawa suka dauki zagayowar ranar sallar bazara a matsayin shekara daya. A shekarar 1,000 da ‘yan doriya, Sinawa sun fara daukar ranar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta manoman kasar bisa matsayin ranar sallar bazara. A wancan zamani, abin da ake nufi da “ Shekara” cikin Sinanci shi ne girbin amfanin gona mai armashi.

Bisa al'adar gargajiya ta Sinawa, su kan shafe makonni uku wato tsakanin ran 23 ga watan Disamba zuwa ran 15 ga watan Janairu bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin suna murnar sallar bazara. A cikin makonin nan uku, Sinawa su kan dauki ranar sabuwar shekara da daren jajibirinta da matukar muhimmanci.

Ko da yake al'adun gargajiya da Sinawa ke murnar sallar bazara sun sha bamban a wurare dabam daban na kasar, amma a daren jajibirin ranar sabuwar shekara, ko shakka babu duk ‘yan ko wane iyali su kan taru gu daya su ci abincin dare tare. A kudancin kasar Sin, mutane su kan dafa kayayyakin lambu iri iri har da yawansu ya kan wuce 10. A arewacen kasar kuma mutane su kan ci kayayyakin fulawa kamar “Jiaozi” da sauransu.

A daren jajibirin ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin, mutane ba sa yin barci, su kan jira zuwan ranar sabuwar shekara. A da, mutane su kan yi wasan wuta a daren don wai neman kore aljanu, amma yanzu, an hana su yi haka a cikin birnin Beijing da sauran manyan birane, domin kare lafiyar jikunansu da hana su kazantar da muhalli. A ranar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar Sin, maza da mata, manya da yara su kan ci ado, su yi maraba da zuwan baki, ko bakunci sauransu don gaida juna.

Sinawa su kan shirya bukukuwan nishadi iri dabam daban. A cikin ‘yan shekarun nan da suka wuce, mutane da yawa su kan je gidajen simina don kallon sabbin sinima da aka dauka musamman domin murnar sallar bazara. A kauyuka, a kan gabatar da wasannin kwaikwayo da wasannin raye-raye da shagugulan bikin salla da makamantasu don taya wa juna murnar sallar bazara. Lalle mutane masu dimbin yawa su kan zauna a gidaje suna kallon shirye-shirye masu ban sha'awa na televijin wadanda aka shirya musamman domin shere su a lokacin bikin sallar bazara. Ban da wadannan bisa kyautatuwar zaman rayuwarsu, Sinawa da yawa su kan yi yawon shakatawa a kasashen waje. Bisa labarin da aka samu daga hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta birnin Beijing, an ce, yawan kudi da ake kashewa wajen yin yawon shakatawa a lokacin sallar bazara yana ta karuwa a ko wane shekara.

Abin da ya cancanta mu ambata a nan shi ne, kasar Sin kasa ce mai yawan kabilu. Ban da kabilar Han, kuma akwai kananan kabilu 55 wadanda ke zaune a kasar Sin. Ko da yake harsunansu da rubutunsu da hanyoyin zaman rayuwarsu da kuma tsabi'unsu ba daya ba ne, amma duk da haka yawancinsu suna daukar sallar bazara da matukar muhimmaci, su kan yi murnar sallar nan daidai kamar yadda suke murnar babbar sallarsu. Alal misali, kabilar Orogen da ta Daur da Korea da Miao da Yao da she da Jing da kuma sauransu su ma su kan shirya shagulgulansu na halayen musamman don murnar sallar bazara.