Yin ziyara a Nanjing a lokacin hunturu

Yau mu yi yawon shakatawa tare da ku a birnin Nanjing wanda ya taba zama babban birnin kasar a cikin dauloli shida cikin tarihin kasar Sin. Birnin Nanjing shi ne hedkwatar lardin Jiangsu, yana da shahararrun wuraren yawon shakatawa da yawa, alal misali, gidan ibada na Confucius, inda za a iya kallon fitilu masu kyan gani, da kuma dandana abinci mai sigar musamman na birnin Nanjing don jin dadin al'adun musamman na mutanen birnin Nanjing a lokacin bikin bazara.

Tarihin birnin Nanjing ya kai shekaru fiye da dubu 2 da dari 4. Idan an isa birnin Nanjing , ya dace a je gidan ibada na Confucius, wanda aka gina shi don tunawa da Confucius, kwararre a fannin ba da ilmi na kasar Sin.

An gina gidan ibada na Confucius a shekarar 1034, tsawon tarihinsa ya kai kimanin dubu daya. Yanzu, gidan ibada na Confucius ya shahara a kasar Sin da kuma kasashen ketare bisa matsayin kyakkyawan wuri na yawon shakatawa. A lokacin bikin bazara na kowace shekara, kallon fitilu masu kyan gani a gidan ibada na Confucius ya riga ya zama wani muhimmin kashi ga mutanen birnin Nanjing da kuma masu yawon shakatawa. Ranar bikin bazara na shekarar 2009 na karatowa, wadanne wasu sabbin aikace-aikace ne kuma za a yi a bikin fitilu na birnin Nanjing da aka taba yi har sau 23? Mataimakin direktan ofishin kula da aikin yankin tsaunukan Qinling da kogin Huaihe na gidan ibada na Confucius Mr. Huan Jianjun ya gabatar da cewa,“A ranakun bikin bazara, idan ba a kallaci fitilu masu kyan gani a gidan ibada na Confucius ba, ba za a ce an taya murnar bikin bazara ba. Muna yin nazari sosai don yin gyare-gyare a bikin nuna filitu a kowace shekara. A shekarar bana, za mu yi gasar fitilu tare da kwamitin kwararru a harkar fitilu na kasar Sin, inda za a tara kyawawan fitilu a nan, alal misali, fitilu iri-iri masu kyan gani na birnin Nanjing da na birnin Taiyuan na lardin Shanxi da kuma na birnin Zigong na lardin Sichuan da dai sauransu, a sa'I daya, muna tuntubar kasar Japan da kuma sauran kasashe don shigo da fitilunsu a yayin bikin.”

Bikin nunin fitilu na birnin Nanjing yana da dogon tarihi, kuma yana samun goyon baya sosai daga al'adun gargajiya, shi ya sa, aka mai da shi a matsayin fasahar da aka gada daga kaka da kakanni na kasar Sin. Da maraice, mutane tare da yaransu sun dauki fitilu masu sigogin shanu da kuma zomo don taya murnar bikin bazara. Masu yawon shakatawa sun iya zaben wani dakin cin abinci dake kan tituna, inda za su iya cin nau'o'in abinci iri daban daban masu dadin ci na birnin tare da kallon fitilu masu kyan gani.

A gabar kogin Huaihe na birnin Nanjing , akwai dakunan cin abinci da yawa. Tarihin galibinsu ya kai tsawon shekaru fiye da dari daya, dakin cin abinci mai suna Qi Fangge yana daya daga cikinsu. A shekarar 2001, Qi Fangge ya samar da kayayyakin tande-tande ga taron Sinawa ‘yan kasuwa a karo na shida, inda baki kimanin dubu 5 na yankuna daban daban na duniya suka dandana cincin iri-iri na birnin Nanjing . Wannan ya sa cincin din birnin Nanjing su shahara a duniya. Shugaban kamfanin abinci na gidan ibada na Confucius na birnin Nanjing Lu Haibo ya gabatar da cewa, “Cincin iri-iri na birnin Nanjing sun nuna fifiko sosai a tsakanin abinci iri-iri na kasar Sin, kuma suna da sigogi da dama.”

Huan Jianjun, mataimakin direktan ofishin kula da aikin yankin tsaunukan Qinling da kogin Huaihe na gidan ibada na Confucius ya ce, “A wurin yawon shakatawa na gidan ibada na Confucius, ba ma kawai ana iya shan iska a gidan ibada na Confucius ba, hatta ma ana iya ganin dakunan cin abinci da yawa, inda za a dandana abinci iri-iri masu dadin ci.

Har ila yau, an kafa wani titin sayar da kayayyaki a yankin gidan ibada na Confucius, inda aka iya sayen zane-zane da kayayyakin tarihi da furani da tsuntsaye da kifaye da kuma sauransu, sabo da haka, wannan titi ya zama cibiyar kasuwanci ta birnin Nanjing. Matsakaicin yawan mutanen da suka yi yawon shakatawa a wannan titi a kowace rana ya haura dubu 100, kuma wannan adadi ya kai kimanin dubu 300 a ranakun hutu. Ban da wannan kuma, hukumar kula da aikin yawon shakatawa ta kasar Sin ta gabatar da gidan ibada na Confucius ga duniya, wannan ya sa karin mutanen kasashen waje suka san wannan shahararren wuri. A lokacin da bikin bazara ya zo mana, a madadin mutanen kasar Sin, maraba da zuwa birnin Nanjing da kuma gidan ibada na Confucius.