Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyarar aiki yankin Tibet a ran 21 ga wata, inda ya yi rangadi kan babbar gadar kogin Niyang don fahimtar yadda ake kiyaye muhallin halittun sassan da kogin Yarlung Zangbo da na Niyang suka ratsa.
An shigar da yankin kiyaye muhallin halittu na mafarin kogin Yarlung Zangbo a cikin rukuni na biyu na yankunan gwaji na kiyaye muhallin halittu a shekarar 2001, inda aka kafa wuraren kiyaye muhallin halittu guda 24 da fadinsu ya kai muraba’in kilomita dubu 1035, da kuma kafa lambunan shan isaka na fadama 12.
A yammacin wannan rana, bi da bi ne Xi Jinping ya kai ziyara dakin tsara shirin raya birnin Linzhi da kauyen Gala da ke yankin Bayi, da lambun shan iska na Gongbu, don ganewa idonsa yadda ake tsara shirin raya birane da raya kauyuka da gina lambunan shan iska a birane da sauransu. A ran 22 da safe kuma, Xi Jinping ya kai ziyara tashar jiragen kasa na Linzhi don ganin yadda shirin shimfida layin dogo tsakanin Sichuan da Tibet ke gudana da yadda ake gudanar da layin dogon dake tsakanin Linzhi da Lhasa da saurasu, daga baya ya tafi Lhasa ta jirgin kasa don yin rangadin wurare da layin dogon ya ratsa. (Amina Xu)