Kasar Sin Ta Samar Da Sama Da Alluran COVID-19 Miliyan 480 Ga Duniya

CRI2021-07-02 20:53:45

Kasar Sin Ta Samar Da Sama Da Alluran COVID-19 Miliyan 480 Ga Duniya_fororder_sin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, kasarsa ta samar da sama da alluran COVID-19 miliyan 480 ga duniya. Yana mai cewa, kasar Sin ta yi imani kan alluran COVID-19 su zama kayan al’ummar duniya, ta kuma samar da galibin alluran ga duniya.

Wang ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kasar Sin, ta samar da alluran ga kasashe kimanin 100, ta kuma yi alkawarin samar da kashin farko na allurai miliyan 10 ga shirin COVAX.

Jami’in na kasar Sin ya ce, alluran riga kafin kasar Sin, su ne na farko da kasashe da dama suka samu. Haka kuma kasar Sin ta yi hadin gwiwa wajen gudanar da bincike da hada riga kafin da samar da shi cikin hadin gwiwa da kasashe masu tasowa da dama, ta kuma taimaka wa kamfanonin da abin ya shafa, wajen yin hadin gwiwa da sassa na ketare wajen gudanar da gwajin alluran a mataki na uku.

Ya kuma bayyana kudirin kasar Sin, na ci gaba da ba da gudummawa wajen ganin kasashe masu tasowa, sun samu riga kafin cikin sauki da kuma rahusa. A don haka, kakakin ya bukaci dukkan kasashe dake da karfi, da su hanzarta daukar mataki, su cika alkawuransu, su taimaka wajen ganin an raba riga kafin, a kuma yi amfani da shi daidai-wadaida tsakanin sassan duniya.(Ibrahim)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)