A kwanakin baya, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, da majalisun dokokin wasu kasashen Afirka hudu, ciki har da Laberiya, da Namibiya, da Afirka ta Kudu da Zimbabwe, sun kaddamar da wani taron sanin makamar aiki ta kafar intanet, mai taken “rawar da majalisun dokoki suke takawa a fannin rage talauci da samar da ci gaba”.
Ta la’akari da yadda aka gudanar da taron, a kusa da lokacin da ake bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS, wasu ’yan majalisun dokoki na kasashen Afirka mahalarta taron sun bayyana ra’ayinsu dangane da JKS.