Wang Yi ya yi kira da a rungumi hanya mafi dacewa ta wanzar da aminci da hadin gwiwa tsakanin Sin da India

CRI2021-02-26 09:59:04

Dan majalissar gudanarwa, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya kira da a rungumi hanya mafi dacewa, ta wanzar da aminci, da hadin gwiwa tsakanin Sin da India.

Wang, ya ce a matsayin kasashen biyu na makwaftan juna, kamata ya yi Sin da India, su hada kai, tare da kauracewa fito ta fito, da zargin juna, da bin hanyoyin da za su gurgunta alakar su.

Ministan harkokin wajen kasar ta Sin, ya yi wannan tsokaci ne, yayin zantawar sa ta wayar tarho da takwaransa na India Subrahmanyam Jaishankar a jiya Alhamis, yana mai cewa, wajibi ne sassan biyu su wanzar da yarjeniyoyin da shugabannin kasashen su suka cimma. Daga nan sai ya bayyana bukatar warware sabanin dake akwai tsakanin Sin da India, game da batun kan iyakar su cikin lumana, domin kaucewa wargaza huldar diflomasiyyar dake tsakanin su.

A cewar jami’in na Sin, a baya bayan nan, India ta dauki wasu matakai na warware wasu sassa na manufofin ta game da Sin, matakin da ya haifar da rashin jituwa, da sabani a fannin hadin gwiwar kasashen, wanda kuma ko shakka babu, hakan zai lahanta moriyar sassan biyu.

Ya ce bisa darussan tarihi, dukkanin wasu matakan rura wutar sabani, ba za su taimaka wajen warware rashin fahimtar juna ba, sai dai ma su zaizaye tushen dangantakar sassan, wadda aka gina kan ginshikin amincewa da juna.  (Saminu)

Not Found!(404)