Maraba da zuwa Wuhan

CRI2021-04-08 21:08:42

A yau ne, birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin, ke cika shekara guda da kawo karshen kangiyar da aka sanya masa. Kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya shaidawa taron manema labaran da aka saba shiryawa Alhamis din nan. Yana mai cewa, al’ummar Wuhan, sun nunawa duniya, karfi da jajurcewar kasar Sin, sun kuma nuna kishi da hadin kan kasar Sin da daukacin al’ummarta na taimakawa juna a duk lokacin da aka shiga wata wahala.

A ranar 23 ga watan Janairun shekarar 2020 ne aka rufe duk wasu hanyoyi na shiga birnin Wuhan, a kokarin ganin an magance yaduwar annobar COVID-19. Sai dai da misalin karfe 12 na daren ranar 8 ga watan Afrilun shekarar 2020, an dage matakan kullen da aka sanya na hana shiga birnin da ma lardin Hubei.(Ibrahim)

—  相关新闻  —

Not Found!(404)