WHO: Binciken asalin COVID-19 a Wuhan aiki ne mai cin gashin kansa

CRI2021-02-16 16:15:38

Babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce binciken asalin COVID-19 a birnin Wuhan da kwararrun hukumar suka yi, aiki ne mai cin gashin kan sa.

Dr. Tedros ya bayyana hakan ne a jiya Litinin ta kafar bidiyo, daga birnin Geneva, yana mai cewa aikin na kwararru mai kunshe da masana daga cibiyoyin ilimin kimiyya 10, ba shi da nasaba da wani bangare na daban.

A jiya Litinin, yayin taron manema labarai, Dr. Peter Ben Embarek, wanda ya jagorantar tawagar kwararrun da suka yi aikin bincike a Wuhan, ya bayyana cewa, rahoton aikin su zai zamo wanda dukkanin su za su amince da shi.

Dr. Embarek ya ce tawagar su, mai kunshe da kwararrun kasa da kasa su 17, da takwarorin su Sinawa 17, ta yi aiki ne tare, gabanin wallafa rahoton hadin gwiwa na wucin gadi, wanda a cikin sa za su gabatar da shawarwari da za su taimakawa sauran bincike da za a yi a nan gaba.

Kaza lika jami’in ya bayyana cewa, akwai bukatar karin bincike mai zurfi, da zai warware sauran batutuwa masu nasaba da tushen wannan annoba.

A farkon wannan wata ne dai tawagar kwararrun na kasa da kasa, ta kammala aikin wata guda na bincike a Wuhan, kana ta gabatar da bayanai masu alaka da aikin, yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a Sin, inda a lokacin ne suka tabbatar wa duniya cewa, cutar ba daga dakin gwaji dake Wuhan ta bullo ba. (Saminu)

404 Not Found

404 Not Found


nginx