Sanin kowa ne cewa, ya kamata a motsa jiki yadda ya kamata. Kwanan baya, masu nazari daga kasar Amurka sun yi kashedi cewa, idan matasa suka motsa jiki mai tsanani domin samun kwanji, to, watakila zai jirkita yanayinsu na cin abinci. Har ma mai yiwuwa za su gamu da matsalar tsayawar bugun zuciya.
Masu nazarin sun gabatar da rahoton nazarinsu cikin mujallar kasa da kasa dangane da matsalar cin abinci, inda suka yi nuni da cewa, wasu matasa sun dauki tsattsauran matakai wajen cin abinci, a kokarin samun kwanji, ba su cin nama da sinadaran kara kuzari, sun kuma tilasta kansu motsa jiki da yawa, suna lura da siffofin jikinsu fiye da yadda ake bukata, lamarin da kila zai jirkita yanayinsu na cin abinci. A wasu lokuta kuma za su gamu da matsalar tsayawar bugun zuciya sakamakon matsalar karancin abinci da kuma motsa jiki fiye da yadda ake bukata. Ban da haka kuma, idan ba su ci abinci yadda ya kamata ba, to, watakila za su fuskanci matsala rashin mu’amala da mutane da kuma kamuwa da ciwon bakin ciki.
Masu nazarin sun dauki shekaru 7 suna gudanar da nazarinsu kan matasa Amurkawa 14891 wadanda shekarunsu suka wuce 11 amma ba su kai 19 a duniya ba. Sun gano cewa, motsa jiki mai tsanani domin samun kwanji ya jirkita yanayin cin abinci tsakanin matasa maza da yawansu ya kai kaso 22 da kuma ‘yan mata da yawansu ya kai kaso 5. Wadannan mutane sun ci abinci da yawa ko kuma ta hanyar da ba ta dace ba, ko cin abubuwa masu dauke da sinadaran da ke gina jiki, ko kuma magunguna masu dauke da sinadarin Hormone, a kokarin kara nauyin jikinsu ko kuma samun kwanji.
Dangane da lamarin, Zhang Chuji, wata likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, gwamnatoci ba su fara sa ido kan abubuwa masu dauke da sinadaran da ke gina jiki ba tukuna. A wasu lokuta cin irin wadannan abubuwa zai illata hanta da koda. Kana kuma magunguna masu dauke da sinadarin Hormone su kan haddasa matsala ga lafiyar mutane cikin gajeren lokaci da ma dogon lokaci, alal misali, shanyewar golo, matsalar girma da ciwon zuciya da dai sauransu.
Har ila yau kuma motsa jiki mai tsanani domin samun kwanji ya kan dauki tsawon lokaci, ta haka zai rage tsawon lokacin mu’amala da mutane, lamarin da yake da nasaba da matsalar mu’amala da mutane da kuma kamuwa da ciwon bakin ciki. Yanzu haka mutanen da suke neman samun kwanji suna motsa jiki ne domin kyautata lafiyarsu, don haka da kyar a gano matsalar da suke fuskanta wajen cin abinci. (Tasallah Yuan)