Jiya Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya je Zhangjiakou don duba ayyukan shirya bikin wasannin motsa jiki na Olympic na lokacin hunturu da na nakasassu da Beijing zai karbi bakunci, inda ya sha jaddada muhimmancin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha
Yayin da ya ziyarci cibiyar wasan tsallen zamiyar kankara mai taushi, Xi ya yi na’am da cewa, ‘yan wasa na amfani da tsarin kwaikwayon tunanin dan-Adam, wajen kyautata samun horo. Ya ce, kamata ya yi a yi amfani da kimiyya da fasaha don raya wasan kankara kamar yadda ake raya kasa, a hannu guda kuma, yana da kyau matuka a dogaro da karfin kirkire-kirkire a fannin samun horo, da koyi da nagargattun dabaru da matakai daga sauran kasashe.
Lokacin da ya ziyarci cibiyar wasan gudun kankara mai taushi tsakanin duwatsu da wasan harbe-harbe na lokacin hunturu, Xi ya nuna cewa, har yanzu akwai ragowar sama da shekara daya da wani abu kafin a gudanar da gasar ta Beijing. Amma an kammala gina duk dakunan wasanni, har ma an fara amfani da layin dogo tsakanin Beijing da Zhangjiakou da kuma tagwayen hanyoyin mota tsakanin Beijing da Chongli. Duk wadannan ayyuka da aka yi musamman ma wasu daga cikinsu suna sahun gaba a duniya, inda suka nuna ci gaban tsare-tsaren kasar Sin. (Amina Xu)