Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya shaida mana cewa, watakila yin dara da kati kullum za su taimaka wa tsoffafi wajen rage saurin samun matsalar rashin fahimta.
Masu nazari daga jami’ar Edinburgh ta kasar Birtaniya sun kaddamar da rahoton nazarinsu cikin mujallar ilmin likitanci dangane da cututtukan tsoffafi, inda a cewarsu, sun gayyaci mutane fiye da dubu 1 wadanda aka haife su a shekarar 1936, dake zaune a Scotland, don su shiga nazarin. Masu nazarin sun gudanar da jarrabawa kan kwarewar wadannan mutane ta fannonin adana abubuwa a kwakwalwa, daidaita batutuwa, saurin yin tunani, a lokacin da shekarunsu suka kai 70, 73, 76, 79 da haihuwa. Ban da haka kuma, masu nazarin sun kara saninsu kan sau nawa ne wadannan mutane suka yi dara da katin wasa, wasan chess da wasan cika gurbi da kalmomi, a lokacin da shekarunsu suka kai 70 da 76 da haihuwa.
Bisa la’akari da ilmin da suka samu, matsayinsu a zaman al’ummar kasa, jinsinsu, makin da suka samu a jarrabawar kwarewar fahimta a lokacin da shekarunsu suka kai 11 da haihuwa, masu nazarin sun yi amfani da dabarar kididdiga, sun tantance alakar da ke tsakanin matsayin wadannan mutane na yin dara da kati da kuma kwarewarsu ta fahimta. An gano cewa, a lokacin da shekarun wadannan mutane suka kai 70 a duniya, idan sun iya yin dara da kati, to, kwarewarsu ta fahimta ta fi ta sauran kyau. A lokacin da wadannan mutane suka tsufa, har shekarunsu suka kai 79 a duniya, idan suka kara yin dara da kati, to, saurin raguwar kwarewarsu ta fahimta zai ragu, musamman ma a fannin adana abubuwa a kwakwalwa.
Masu nazarin sun kuma gano cewa, idan wasu sun kara yin dara da kati a lokacin da shekarunsu suka wuce 70 amma ba su kai 77 a duniya, to, za su rage saurin rashin fahimtarsu. Ma iya cewa, duk da ba safai akan yi dara da kati a kullum a baya ba, idan an fara yin dara da kati yayin da aka fara tsufa, to, zata amfana wa lafiyar mutane.
Masu nazarin su yi karin bayani da cewa, nazarin da suka gudanar ya taimaka wajen kara fahimta kan wani irin salon zaman rayuwa da harkokin da tsoffafi suka yi ke da amfani wajen kyautata kwarewar fahimtarsu. Har ila yau kuma nazarin ya ilmantar da mutane dangane da yadda za a kare kwarewar fahimta yadda ya kamata yayin da aka tsufa. (Tasallah Yuan)