Jami’an lafiyar Afrika ta kudu suna maraba da yunkurin AU na neman riga-kafin COVID-19

CRI2021-01-15 10:36:23

Kungiyar gamayyar ma’aikatan ilmi da na lafiyar kasar Afrika ta kudu NEHAWU, tana maraba da yunkurin kungiyar tarayyar Afrika AU wajen nemo alluran riga-kafin annobar COVID-19, kana ta bukaci kasashen su bayar da fifiko ga ma’aikatan kiwon lafiya.

NEHAWU tana maida martani ne kan sanarwar da shugaban kungiyar ta AU Cyril Ramaphosa ya fitar a daren Laraba cewar, nahiyar ta samar da riga-kafin kimanin miliyan 270.

Ramaphosa ya bukaci gwamnatoci dasu yaki da masu neman yada jita-jita da nufin jan halin mutane kauracewa karbar riga-kafin.

 

Ya gargadi mutane cewa kada su damu kasancewar riga-kafin yana nan tafe, kana ya bukaci mutane su cigaba da kiyaye matakan kariyar daga annobar ta COVID-19, ta hanyar bayar da tazara, da amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta, da sanya takunkumin rufe fuska.(Ahmad)

Not Found!(404)