Rahotanni daga kasar Morocco na cewa, sojojin ruwa dake tsaron gabar ruwan kasar, sun yi nasara kwace sama da tan uku na tabar Wiwi ranar Asabar a tekun Bahar Rum.
Kamfanin dillancin labaran kasar ya bayyana cewa, masu tsaron gabar ruwan kasar, sun tare wasu kwale-kwale guda biyu da ake zargi da sumogan tan 3 na kayayyakin tabar wiwi zuwa yankin ruwayen dake kusa da birnin Mdiq dake arewacin kasar.
Yanzu haka dai, an damkawa hukumomi kayayyakin da aka kama har ma sashen shari’ar kasar ya fara gudanar da bincike a kan lamari.
Ana dai safarar galibin tabar wiwin da ake nomawa a wasu yankunan kasar ta Morocco da yanzu haka lamarin ya yi kamari ne zuwa Turai. A cikin sama da shekaru goma da suka gabata, dakarun tsaron kasar Morocco, sun kara kaimi wajen dakile yadda ake noma da cinikin tabar wiwi, inda a shekarar 2019 kadai, aka kama kusan tan 179 na tabar wiwi.(Ibrahim)