Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron warware takaddamar siyasar kasar Libya
2020-11-10 10:00:45        cri

A jiya Litinin ne aka kaddamar da taron warware rikicin siyasar da ya dade yana addabar kasar Libya a birnin Tunis na kasar Tunisia. Shugaban kasar Tunisia Kais Saied ne ya ayyana bude taron na yini 6, a gaban wakiliyar musamman ta babban magatakardar MDD a kasar Libya Stephanie Williams, da wasu wakilan musamman 75 da MDD ta zaba domin sanya ido.

Da take tsokaci yayin bude taron mai lakabin LPDF, uwargida Stephanie Williams, ta ce sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da bude wuta a daukacin sassan kasar Libya suka amincewa, shi ne ya samar da damar halartar taron na wannan karo ga dukkanin masu ruwa da tsaki, duk kuwa da yanayin da ake ciki na matakan yaki da cutar COVID-19 a Libya, da Tunisia da ma sauran sassan duniya.

Williams ta kuma bayyana kyakkyawan fatan ganin dukkanin sassan masu ruwa da tsaki a Libya sun shiga an dama da su a wannan dandali, don kaiwa ga matakin warware sabani, da cimma matsaya guda.

Shi kuwa shugaba Kais Saied, jaddada matsayar sa ya yi game da baiwa al'ummar Libya, damar warware rashin jituwar su, yana mai cewa su kadai ne ke iya shawo kan matsalar kasar su, bisa yardar daukacin al'ummar ta. Ya ce dandalin LPDF na fatan kaiwa ga matakin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Libya.

Taron LPDF ya hallara daukacin masu ruwa da tsaki a siyasar kasar Libya, an kuma tsara gudanar sa ne yayin taron birnin Berlin, wanda ya samu amincewar kudurin kwamitin tsaron MDD mai lamba ta 2510 da mai lamba 2542 na shekarar 2020, kamar dai yadda wata sanarwa da tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya, ko UNSMIL ta tabbatar da hakan. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China