2020-11-09 16:32:25 cri |
An yi amfani da shekaru 30 wajen canja yankin daga filayen gona zuwa manyan gine-gine. A shekarar 2019, yawan GDP na yankin Pudong ya kai Yuan biliyan 1273.4, wanda ya karu tare da ninkawa har sau 211 bisa na shekaru 30 da suka gabata.
A wannan yanki, akwai gini na biyu mafi tsawo a duniya wato ginin cibiyar Shanghai, tsawon ginin mai hawa 132, ya kai mita 632, fadinsa kuma ya kai murabba'in mita dubu 578.
A halin yanzu, akwai manyan gine-gine 285 a yankin Pudong, guda 97 daga cikinsu, sun biya harajin fiye da Yuan miliyan 100, kwatankwacin yawan tattalin arzikin wata gunduma a kasar Sin, hakan ya kafa al'ajabi bayan da aka gudanar da manufofin yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin.
An shiga sabon lokaci, yankin Pudong zai kara samun ci gaba. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China