Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dokar tattara shara a gidaje ta birnin Shanghai ta fara aiki
2019-07-02 11:16:08        cri

An kaddamar da wasu ka'idoji na kula da tattara shara a gidaje a birnin Shanghai, dokar wacce ta fara aiki a ranar Litinin, sama da sanarwar gargadi 600 aka amince dasu wadanda aka aikewa daidaikun mutane, kamfanoni da kuma cibiyoyi a ranar farko da dokar ta fara aiki.

Otel din five-star, wanda ke tsakiyar birnin Shanghai, an mika masa kofen takardar gargadi da safiyar ranar Litinin sakamakon gazawar da yayi wajen tara shara a muhallin da ya dace.

Hukumomin tsara dokoki na birnin sun ziyarci yankuna kusan 1,600, da kamfanoni sama da 400, da kuma shaguna sama da 1,800 da otel otel 21, inda suka gabatar da takardun gargadi don a yi gyara guda 623 tare da bayyana hukunci ga duk magidantan da suka saba sabuwar dokar tattara sharar ta birnin, kamar yadda hukumar tsara dokoki da raya birnin Shanghai ta bayyana.

Hukumar kula da birnin ta kuma wallafa sunayen jami'ai na musamman 20 da zasu dinga sanya ido a guraren tara shara na gidaje, wadanda zasu dinga kai ziyarar ba zata a yankunan gidajen al'umma, da asibitoci da kuma makarantu, har ma da yadda ake jigilar sharar a gundumomi 16 na birnin Shanghai. Ana sa ran a nan gaba za'a kara yawan jami'an masu sanya ido.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China