Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani harin bom ya yi sanadin mutuwar mutane biyu a Afghanistan
2020-11-09 14:03:54        cri
Mutane akalla biyu, ciki har da maharin, sun mutu, yayin da wasu 16 suka jikkata, sanadiyyar wani harin bom da aka kai cikin mota a gudumar Maiwand na lardin Kandahar na kasar Afghanistan jiya da dare.

Wasu majiyoyi sun shaida cewa, lamarin ya auku ne bayan wani dan kunar bakin wake cikin mota ya farwa wani sansanin 'yan sanda dake kusa da gundumar Bazaar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 13 da raunata wasu 33.

Sun ce adadin wadanda harin ya rutsa da su ka iya karuwa, bisa la'akari da yadda bam din ya lalata gine-ginen sansanin da gidaje a shagunan dake kusa.

Kawo yanzu, babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

A wani labarin kuma, yara da mata 8 sun mutu yayin da wasu 7 suka jikkata, bayan hare-hare 3 da 'yan Taliban suka kai sansanin 'yan sanda a Ghazni, babban birnin lardin Ghazni dake gabashin kasar da yammacin jiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China