Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a helkwatar 'yan sanda a Afghanistan
2020-10-19 09:31:21        cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da babbar murya game da mummunan harin da aka kaddamar kan helkwatar hukumar 'yan sanda a lardin Ghor na kasar Afghanistan.

A sanarwar da kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya fitar, ya ce an kaddamar da mummunan harin na lardin Ghor ne a wani yankin da fararen hula masu yawa ke zama.

Rahotannin farko sun nuna cewa, harin yayi sanadiyyar hallaka rayuka 13 da kuma jikkata fararen hula masu yawa, wanda ya hada da mata da kananan yara. Sanarwar tace tilas ne a hukunta mutanen dake da hannu wajen shirya kai harin.

Babban sakataren ya bayyana tausayi da kuma jajantawa iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da fatan samun sauki ga mutanen da suka samu raunuka a harin. Kana sanarwar tace, MDD a shirye take ta taimakawa jama'a da gwamnatin kasar ta Afghanistan.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China