Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Darajar hidimomin da za a shigo da su kasar a shekaru 5 masu zuwa za ta kai dala triliyan 2.5
2020-11-07 17:20:46        cri

Ma'aikatar kula da kasuwanci ta kasar Sin ta fitar da "rahoton hidimomin da ake shigo da su kasar Sin daga ketare na shekarar 2020" yayin bikin CIIE wato baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar daga ketare karo na uku, inda aka yi hasashen cewa, sakamakon matakan kara bude kasuwar hidimomi da gwamnatin kasar ta dauka, a cikin shekaru biyar masu zuwa, ana sa ran darajar hidimomin da za a shigo da su kasar Sin daga ketare za ta kai dalar Amurka triliyan 2.5, jimillar da za ta kai kaso sama da 10 bisa dari dake cikin daukacin hidimomi a fadin duniya a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Rahoton ya nuna cewa, tun bayan da kasar Sin ta shiga hukumar cinikayya ta duniya a shekarar 2001, jimillar hidimomin da suka shigo kasar daga ketare ta kai dala triliyan 4.7, wadda ke karuwa da kaso 15.2 bisa dari a ko wace shekara, wato ta fi karuwar kaso 7.7 bisa dari na matsakacin matsayin duniya a cikin wadannan shekaru masu yawa, ana iya cewa, ta taka babbar rawa kan karuwar shigowar hidimomi tsakanin kasa da kasa.

Kuma bankin duniya da wasu hukumomin MDD sun yi hasashen cewa, a shekarar 2019, kasar Sin ta samar da guraben ayyukan yi sama da miliyan 18 ga abokan cinikayyarta ta hanyar shigowa da hidimomi daga ketare, a ciki, guraben ayyukan yi da ta samar wa kasashen Afirka sun kai dubu 400, kana guraben ayyukan yi da ta samar wa kasashen da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya sun kai miliyan 3.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China