Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara yawan kudin da take kashewa da nufin kyautata rayuwar al'umma
2020-11-07 17:02:29        cri

Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta yanke shawarar daukar matakan tabbatar da kara kashe kudi da nufin kyautata rayuwar al'ummarta.

Wata sanarwa da aka fitar bayan taron majalisar da ya gudana karkashin jagorancin firaminista Li Keqiang, ta ce majalisar ta kuma shirya inganta gangamin wayar da kai game da kiwon lafiyar al'umma, yayin da ake tsaka da daukar matakan kandagarki da takaita yaduwar COVID-19 da sauran cututtuka a lokacin hunturu.

Taron ya kuma nanata bukatar kara tabbacin rayuwa da daukaka zamantakewar al'umma ta hanyar ba da fifiko ga shirye-shiryen kasafin kudi dake tabbatar da kyautata rayuwarsu da inganta cibiyoyin dake kula da rayuwar jama'a da tabbatar da moriyarsu da dorewar manufofin da jama'a ke cin gajiya.

Da yake bayyana muhimmiyar rawar da gangamin kiwon lafiyar al'umma ke takawa wajen karewa da inganta lafiyar jama'a, taron ya bukaci a yi kwakkwaran aiki wajen kandagarki da takaita annobar akai-akai a lokacin hunturu, tare kuma da inganta tsaftar muhalli a birane da kauyuka.

Har ila yau, taron ya jaddada batun karfafa gina cibiyoyin kula da lafiyar al'umma da na sarrafa shara, da koyar da jama'a yadda za su rungumi dabi'un kula da lafiya da rayuwa cikin koshin lafiya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China