Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Manyan laifuka bakwai da Amurka take aikata suna iya yiwa tsaron duniya barazana
2020-11-05 13:49:48        cri
Halaye marasa dacewa da Amurka take aikatawa, babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron duniya. Ministan harkokin wajen kasar Cuba Bruno Rodrigurz, ya sha bayyanawa a jerin tarukan manyan jami'ai da aka gudanar don murnar cika shekaru 75 da kafuwar MDD a watan Satumba cewa. Gwamnatin Amurka ta aika a kalla munanan laifuka dake iya yin barazana ga tsaron duniya.

Na farko shi ne, tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe da yin barazana ga tasron siyasar duniya. Na biyu, kakabawa kasashe takunkumi babu gaira babu dalili, barazana ce ga tsaron tattalin arzikin duniya. Na uku tseren mallakar makamai shi ma barazana ce ga tsaron ayyukan soja a duniya. Na hudu, kawo tsaiko a kokarin da ake na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli, da yin barazana ga tsarin muhallin duniya. Na biyar, yayata akidar babakere da yin barazana ga tsaron muhallin halittu na duniya. Na shida, aikata kutse ta intanet, da yiwa tsaron muhimman bayanan kasashen duniya barazana. Sai kuma na bakwai kuma na karshe, yiwa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19 zagon kasa da yiwa tsarin lafiyar duniya barazana.

A duniyar ta yau, zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwar moriyar juna, su ne hanyoyin ci gaba. Duk wani ra'ayi na son kai, da babakere, da dagawa, da yi wa wasu matsin lamba, da hadin baki da za su kawo cikas ga hadin gwiwar kasa da kasa da illata tsaron duniya, ba za su taba samun gindin zama ba kuma tarihi zai yi Allah wadai da su.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China