Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi: Dole ne Sin ta aiwatar da dukkanin matakan ci gabanta bisa tsari
2020-11-03 20:42:27        cri

Shugaban kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin aiwatar da dukkanin matakan ci gaban kasarsa bisa tsari, yayin da ake aiwatar da shawarwarin dake kunshe cikin daftarin da kwamitin kolin JKS ya gabatar, na raya tattalin arziki da jin dadin jama'a na shekaru biyar karo na 14, wanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa ta 2025.

Xi ya bayyana hakan ne, cikin jawabin da ya gabatar a Talatar nan, yayin zaman tattaunawa na kwamitin kolin JKS mai aikin tsara shawarwarin da ake fatan amincewa, na shekaru biyar karo na 14, da wadanda ake fatan cimmawa a dogon zango nan da shekarar 2035.

Shugaba Xi ya yi nuni ga irin sauye sauye masu sarkakiya dake faruwa a fannonin ci gaban kasar Sin, da kalubalen rashin daidaito, da karancin bunkasuwa a wasu sassa, da kuma sarkakiyar matsalolin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al'ummar kasar.

Ya ce za a iya warware wadannan batutuwa da matsaloli ne kawai, ta hanyar bin tsari sannu a hankali, ta yadda za a kai ga bunkasa sassa daban daban, da aiwatar da manufofin zamanantar da salon gurguzu a dukkanin fannoni, kuma bisa cikakken tsari. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China