Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in MDD ya nuna damuwa kan hare-hare a Habasha
2020-11-04 09:58:11        cri
Sakatare-janar na MDD Antonio Guterres ya bayyana damuwa game da wasu rahotannin tashin hankali da hare-hare da aka kaddamar kan fararen hula a kasar Habasha, wanda yayi sanadiyyar mummunan hasarar rayuka.

A sanarwa da Dujarric kakakin babban sakataren ya fitar, mista Guterres ya aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda rikicin ya rutsa da su kana ya yi fatan samun sauki cikin hanzari ga mutanen da suka samu raunuka. Ya bukaci a gurfanar da wadanda ke da hannu wajen shiryawa da kaddamar da hare-haren.

Sanarwar ta ce babban sakataren ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki da su dauki matakan gaggawa wajen kwantar da hankulla a kasar, kana a yi kokarin shawo kan kalubalolin ta hanyar hawa teburin tattaunawar sulhu.

Guterres ya jaddada aniyar MDD na goyon bayan gwamnatin kasar Habashan a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da kyautata makomar kasar, wanda hakan zai bada gudunmawa wajen dorewar zaman lafiya da samun dawwamammn ci gaba a shiyyar kahon Afrika.

Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar Habasha ta sanar a ranar Litinin cewa, wasu 'yan bindiga sun kaddamar da hari a yankunan jahar Oromia ta kasar Habasha a ranar Lahadi inda yayi sanadiyyar rayukan mutane 32. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China