Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya da Burtaniya sun kammala tattaunawar da za ta ba su damar yin cinikayya bayan Brexit
2020-11-04 09:35:56        cri
A jiya ne kasashen Kenya da Burtaniya, suka kammala cimma yarjejeniyar hadin gwiwa ta (EPA), wadda za ta baiwa sassan biyu tabbacin gudanar da harkokin cinikayya, bayan da Burtaniyar ta kammala ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai (EU) a ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara.

Babban mai shiga tsakani na kasar Kenya, kana babban sakatare a ma'aikatar raya masana'antu, cinikayya da sana'o'i Johnson Weru da babban mai shiga tsakani a bangaren Burtaniya Paul Walters, sun bayyana cewa, sassan biyu sun cimma matsaya bisa manufa kan yarjejeniyar Kenya da kasashen gabashin Afirka(EAC) da yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki ta Burtaniya.

Jami'in sun bayyana cikin wata sanarwar hadin gwiwa cewa, ana sa ran yarjejeniyar wadda za ta fara aiki a karshen wannan shekara, za ta kawo karshen kudin fito da ake biya na dogon lokaci, da baiwa 'yan kasar Kenya damar shigo da wani kaso na hajojinsu cikin kasar Burtaniya, da ma sauran shiryen-shiryen tattalin arziki da cinikayya da sassan biyu suka kulla.

Bugu da kari, yarjejeniyar, za ta ci gaba da baiwa 'yan kasuwa da masu zuba jari da hanyoyin samar da kayayyaki, damar tafiyar da harkokinsu, za kuma ta samar da wani ginshiki na kara habaka tattalin arziki da Karin damammaki a nan gaba.

Jami'an sun kara da cewa, jami'an gwamnatocin kasasheh biyu, sun fito da wata alakar gajeren sako, dake alamta kawo karshen tattaunawar. Nan da makonni masu zuwa ne dai, za a shirya sanya hannu kafin a gabatar da ita zuwa matakin kasashen na gaba, ciki har da majalisun dokoki domin kammala ragowar shirye-shiryen amincewa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China