2020-11-02 09:51:06 cri |
Shugaban hukumar zaben kasar Mohammed Charfi ya bayyana cewa, hukumarsa za ta kira taron manema labarai Litinin nan don sanar da sakamakon karshe na kuri'un da 'yan kasar suka kada.
An kada kuri'un ne a runfunan zabe 13,236 da aka tanada a sassan kasar daban-daban da kuma wasu tashoshin kada kuri'a 43 dake kasashen waje.
An bukaci 'Yan kasar Aljeriya ne, da su yanke shawara game da yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska kamar yadda shugaba Abdelmadjid Tebboune ya yi alkawari a lokacin yakin neman zabensa.
Akwai wasu ayoyi masu sarkakiya da aka gabatar a shirin yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, ciki har da yiwuwar aika dakarun kasar zuwa kasashen waje a karon farko cikin tarihin kasar, don taimakawa shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya na MDD.
A wani mataki na hana yaduwar cutar COVID-19, hukumar zaben kasar, ta fito da wani shiri na musamman, don tabbatar da cewa, shirin ya gudana cikin nasara, ciki har da ba da tazara da sanya abin rufe baki da hanci da aka bukaci masu kada kuri'a su yi.(Ibrahim)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China