Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeriya da Tunisiya sun tattauna batun rikicin Libya da hadin gwiwar kasashen biyu
2020-02-03 11:05:22        cri
Kamfanin dillancin labarai na APS ya ba da rahoto jiya Lahadi kan cewa, shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya ce kasashen Algeria da Tunisiya sun yi musayar ra'ayoyinsu game da wasu batutuwa dake shafar kasa da kasa da na shiyya, wanda ya kunshi batun rikicin kasar Libya.

Shugaban ya yi tsokaci ne a taron 'yan jaridu na hadin gwiwa tare da takwaransa na kasar Tunisiya Kais Saied wanda ya ziyarci kasar.

Tebboune ya yi alkawarin cewa kasarsa za ta ajiye dala miliyan 150 a bankin kasar Tunisiya a matsayin rance, domin bunkasa tattalin arzikin makwabciyar kasar.

Ya bayyana cewa kasashen Algeria da Tunisia suna musayar ra'ayoyi kan batutuwa dake shafar dukkan fannoni a matakin kasa da kasa da na shiyya wanda ya hada har da batun rikicin Libya.

Ya kara da cewa, dukkan bangarorin biyu sun yarda cewa batun warware rikicin kasar Libya yana hannun 'yan kasar Libyan, inda ya nanata yin gargadi ga bangarorin kasashen ketare su guji yin shisshigi a harkokin cikin gidan kasar kuma su dakatar da safarar makamai zuwa kasar ta Libya.

A nasa bangaren, Saied ya nanata cewa, ya kamata kasashen biyu su bullo da sabbin matakan hadin gwiwa a tsakaninsu wanda za su taimaka wajen cimma muhimman muradun al'ummonin kasashen biyu.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China