2020-10-29 10:18:48 cri |
Wakilan sun bayyana hakan ne a wani taron kafafen yada labarai da suka gudanar ta intanet a ranar Laraba.
A cewar wakilan, ya kamata kafafen yada labaran su yayata hadin gwiwar da Sin da Afrika ke yi a kokarin kawar da annobar, kuma su bayar da gudunmawa wajen farfadowar harkokin tattalin arziki, da kyautata rayuwar al'umma a kasashe masu tasowa bayan annobar.
Taron ya cimma matsayar cewa, kafafen yada labarum za su rungumi tsarin cudanyar bangarori daban daban da kuma gudanar da harkokin su bisa tsarin manufar MDD, kana za su cigaba da goyon bayan hukumar lafiya ta duniya WHO a kokarin yaki da annobar COVID-19.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China