Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Illata dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ba zai sanya "Amurka ta sake girma" ba
2020-07-10 20:25:36        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya ce, duk wani yunkuri na neman bata hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da illata dangantakar dake tsakaninsu, ba zai sanya kasar "Amurka ta sake girma" ba.

Kakakin wanda ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Juma'a, ya ce akwai zarge-zargen da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya yi cewa, wai kasarsa ba ta jin dadi kan hadin kan da kasashen Sin da Rasha suka yi tare da kasashen Afirka a fannin tattalin arziki, tana kuma fatan kasashen Afirka za su fahimci cewa, kasashen Turai da Amurka su ne "ainihin abokan hadin kai". Game da haka, Zhao Lijian ya bayyana cewa, tun bayan bullar annobar COVID-19, Sin da kasashen Afrika sun yi hadin kan da ya dace a fannin dakile annobar. Ban da wannan kuma, a yayin taron kolin musamman na hadin gwiwar yakar cutar COVID-19 a tsakanin Sin da Afirka, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jerin shawarwari da manufofi masu muhimmanci, wadanda suka samu karbuwa sosai daga wajen kasashen Afirka.

Zhao Lijian ya jaddada cewa, ko da yaushe kasar Sin na girmama ra'ayin jama'ar Afirka, da yin la'akari da bukatun kasashen Afirka, kana ba ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashen na Afirka. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China