Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin shiga na mazaunan kauyen Eni na garin Xide ya karu da ninka 2.7 bisa na shekarar 2018
2020-10-28 16:56:06        cri
Ya zuwa yanzu, akwai garuruwa 7 da ba a kawar da talauci a yankin Liangshan na lardin Sichuan ba. Bayan da aka yi kokari a wasu shekaru, kauyen Eni na garin Xide dake yankin Liangshan da tsayinsa ya kai mita 3000 daga teburin teku ya samu babban canji.

Bayan da bangarori daban daban suka yi hadin gwiwa wajen neman yarjejeniyoyi, da kafa tsarin samun bunkasuwa ta yin shuke-shuke, da kiwon dabbobi, da kuma inganta sha'anin shuka 'ya'yan itatuwa na Kaya, da kuma kayayyakin da aka sarrafa magunguna da su a kauyen Eni.

A shekarar bara, an yi amfani da tsarin hadin gwiwar dake tsakanin hukumomin gwamnatin kauyen da kamfanonin hadin gwiwa, da kuma masu fama da talauci, don su yi rajista don taimakawa masu fama da talauci fiye da 100 wajen kawar da talauci.

An samu kyakkyawan sakamako bayan da aka yi kokari. Yawan kudin shiga na kowane mazaunin kauyen Eni ya karu da ninka 2.7 bisa na shekarar 2018, kana yawan kudin shiga na kauyen ya karu da ninka 24. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China