Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram 16 a arewa maso gabashin kasar
2020-10-26 10:53:43        cri

A kalla mayakan Boko Haram 16 sojojin Najeriya suka hallaka a hare hare uku na baya bayan nan da suka kaddamar a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Benard Onyeuku, kakakin rundunar sojojin Najeriyar ya bayyana hakan a wata sanarwar da aka fitar game da nasarorin da rundunar sojojin ta cimma tsakanin ranar Laraba zuwa Asabar, yayin da sojojin suka yi sansani a shiyyar sun fara aikin kakkabe mafakar mayakan na Boko Haram.

Onyeuku ya ce, an tura rundunar sojoji ta musamman zuwa yankin Gajram dake jihar a ranar Laraba, inda aka gano motocin mayakan Boko Haram suna shirin bibiyar ayarin motocin dake daukar mutanen dake zaune a sansanonin 'yan gudun hijira daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin sake mayar da su garin Baga dake makwabtaka da tafkin Chadi.

Dakarun sojojin sun yiwa mayakan Boko Haram kofar rago, inda suka yi musu mummunar barna, a cewar Onyeuku, ya kara da cewa, an kashe mayakan uku a musayar wutar da suka yi da sojojin.

Ya cigaba da cewa, rundunar musamman ta sojoji ta Army Super Camp dake yankin Magumeri, sun yi arangama da mayakan Boko Haram, inda suka kashe 11 daga cikinsu.

Haka zalika, a cewar Onyeuku, sojojin na Army Super Camp dake yankin Mallam Fatori, sun afkawa mayakan 'yan ta'addan na Boko Haram, sun kashe mayakan 2, kana ragowar sun tsere da raunukan harbin bindiga.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China