Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Harin Boko Haram ya kashe 'yan sanda 8 da wasu mutane 3
2020-09-27 16:41:39        cri
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar 'yan sanda 8 da jami'an tsaron civilian JTF 3 da ke samun goyon bayan gwamnati, a wani harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka kaddamar kan ayarin jami'an gwamnatin jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Harin wanda aka kaddamar a ranar Juma'a a kusa da garin Monguno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, a yayin da jami'an gwamnatin ke kan hanyarsu ta zuwa garin Baga inda ake shirin karbar daruruwan 'yan gudun hijira dake shirin sake komawa garuruwansu.

Kakakin 'yan sandan jahar Borno, Edet Okon ya fadawa 'yan jaridu a Maiduguri, babban birnin jahar cewa, lamarin yayi sanadiyyar jikkata wasu mutane 13.

Harin na ranar Juma'a shi ne karo na biyu da aka kaddamar a jahar ta arewacin kasar, wanda yayi matukar tayar da hankula. Yankin Monguno dake jahar Borno an yi amanna yanki ne mai hadarin gaske, kana ya sha fuskantar jerin hare hare da yin garkuwa da mutane daga mayakan 'yan ta'adda.

Kafin wannan, kafafen yada labaran cikin gidan kasar sun bada rahoton cewa, kimanin jami'an tsaron Najeriya 15 da suka hada da 'yan sanda 8, da sojoji uku, da jami'an tsaron sa kai na Civilian JTF hudu ne aka hallaka a harin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China