Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MIIT: Fasahar 5G ta Sin ta nuna kyakkyawan sakamako
2020-10-23 13:44:13        cri

Ma'aikatar masana'antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin MIIT ta ce, cigaban fasahar zamani ta 5G ta kasar Sin ta samar da kyakkyawan sakamako.

Wani jami'in ma'aikatar ta MIIT ya fadawa taron 'yan jaridu a jiya Alhamis cewa, a halin yanzu, kasar Sin tana da tashoshin fasahar 5G sama da 690,000. Kana sama da tashohin 500,000 an gina su ne a shekarar nan ta 2020, har ma an cimma burin da aka kuduri aniya tun gabanin cikar wa'adin da aka diba wanda aka tsara a farkon wannan shekarar, a cewar Wen Ku, jami'in MIIT.

Wen ya ce, adadin wayoyin hannu masu fasahar 5G ta kasar Sin da aka samar daga watan Janairu zuwa Satumba ya kai kusan miliyan 108.

Sakamakon karuwar masu amfani da fashar ta 5G, adadin yawan hanyoyin sadarwar da aka yi amfani da fasahar ya zarce miliyan 160 ya zuwa ranar Litinin din da ta gabata, in ji Wen.

A cewar jami'in, fasahar 5G tana taka muhimmiyar rawa, musamman wajen daidaita tsarin zuba jari, da bunkasa harkokin hada hadar kasuwanci, da kuma kawo sabbin hanyoyin bunkasa cigaban tattalin arziki.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China