Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Akwai sama da tashoshin 5G dubu 200 da ake amfani da su a kasar Sin
2020-05-18 10:59:27        cri

Ma'aikatar masana'antu da fasahohin sadarwa na zamani ta kasar Sin (MIIT) ta bayyana cewa, tashohin fasahar 5G da ake amfani da su a fadin kasar, sun zarce dubu 200.

Mataimakin ministan ma'aikatar Chen Zhaoxiong, shi ne ya bayyana haka, yana mai cewa, kasar Sin tana da kwarewa wajen gina na'urorin Intanet, inda masu amfani da fasahar 4G suka kai miliyan 128.

Chen ya kara da cewa, tattalin arzikin yanar gizo, ya zama sabon karfin samar da ci gaba, inda ya dauki kaso 1 bisa uku na GDPn kasar.

Kamfanin sadarwa na China Mobile, daya daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na kasar, ya ce, zai mallaki tashoshin fasahar 5G sama da dubu 300 nan da karshen shekarar 2020 da muke ciki.

Shi ma kamfanin sadarwa na China Unicom, ya bayyana cewa, zai hada kai da China Telecom don kammala aikin gina tashoshin fasahar 5G dubu 250 a sassa daban-daban na kasar nan da karshen wannan shekara.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China