2020-10-23 11:42:26 cri |
A yau Juma'a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a dauki matakan tabbatar da zaman lafiyar duniya da tabbatar da adalci, ya bayyana hakan ne a taron tunawa da cika shekaru 70 da dakarun sa kai na jamhuriyar jama'ar kasar Sin wato CPV, suka shiga zirin Koriya ta Arewa domin yaki da nuna danniyar Amurka.
Xi Jinping ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki da mutanen duniya domin gina kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.
Kasar Sin ba ta neman yin kama karya, ko neman yiwa wata kasa mamaya, kana tana Allah wadai da nuna karfin tuwo, da amfani da karfin iko ta hanyar siyasa. Kasar Sin ba za ta lamintar duk wani yunkurin amfani da karfi wajen karbe iko ba.(Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China