Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta da alhaki game da matsalolin bashi dake addabar wasu kasashe
2020-10-20 20:06:40        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Sin ba ta da alhaki game da matsalolin bashi dake addabar wasu kasashe kamar Amurka da sauran kasashe masu ci gaba, sakancewar mafi yawan bashin dake wuyan irin wadannan kasashe, sun ciwo su ne daga manyan cibiyoyin ba da lamuni na kasa da kasa.

Jami'in na wannan tsokaci ne, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, inda a yayin taron na yau Talata, ya ce matsalolin bashi dake addabar irin wadannan kasashe, na da nasaba da yanayin gudanar da manufofinsu na raya tattalin arziki, baya ga sauyi da ake samu a yanayin tattalin arziki mai nasaba da manyan sassan cinikayya da lamuni na duniya baki daya.

Zhao ya kara da cewa, ko alakar Sin da wadannan kasashe na da kyau ko a'a, akwai shaidu a bayyana dake tabbatar da matsayin tattalin arzikin su. Kuma ga masu fatan sauya gaskiya, ko kirkirar karairayi da nufin bata sunan kasar Sin, kamata ya yi su yi karatun ta natsu, su dauki sahihan matakai da za su zamo masu alfanu ga sassan kasa da kasa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China