Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping: Karfin kasar Sin daga dukkanin fannoni ya kai sabon matsayi a tarihi
2020-10-22 20:45:58        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, karfin tattalin arzikin kasarsa, da karfinta a fannin kimiyya da fasaha, da ci gaban kasa daga dukkanin fannoni, sun kai sabon matsayi, tun bayan fara aiwatar da shirin raya kasa na shekaru 5 kaso 13.

Shugaban na Sin ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, lokacin da yake jagorantar taron zaunannen kwamitin siyasa na kwamitin kolin JKS, don sauraron rahoton aiwatar da shirin na raya kasa na shekaru 5 kasor 13.

Shirin dai ya kunshi kudurorin ci gaba na kasar Sin masu nasaba da tattalin arziki, da raya zamantakewar al'ummar kasar. Kana yana kuma kunshe da manyan ayyukan gine-gine na bunkasa kasa, da rarraba karfin sarrafa hajoji, da dabarun rarraba sassan tattalin arziki, tsakanin shekarun 2016 zuwa 2020. Kaza lika ya kunshi burika, da hanyoyin cimma nasarar kudurorin kara raya tattalin arzikin kasar ta Sin cikin shekarun 5.

Yayin taron na yau, an jaddada cewa, a lokacin aiwatar da kudurorin ci gaba na shekaru 5 karo na 14, Sin za ta shiga sabon mataki na bunkasuwa. Za ta kara azama kan aniyarta, kana za ta bude sabon mafari na gina salon gurguzu na zamani daga dukkanin fannonin rayuwa. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China