Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi kira da juriya wajen yaki da talauci
2020-10-17 16:04:23        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya nanata bukatar juriya da jajircewar kasar yayin da take kokarin cin nasara a yaki da talauci.

Cikin wani umarni da shugaban ya bayar yayin da kasar ke gudanar da ranar yaki da talauci karo na 7 da ake yi a duk ranar 17 ga watan Oktoba, ya ce dole ne kwamitocin jam'iyya da gwamnatoci a dukkan matakai, su ci gaba da aikin yaki da ake da talauci ba tare da kasa a gwiwa ba, har sai an cimma nasara baki daya.

Shugaba Xi ya ce 2020, ita ce shekarar da kasar Sin za ta kammala gina al'umma mai matsakaicin ci gaba a dukkan fannoni tare da kawo karshen talauci a kasar.

Ya ce yayin da ake fuskantar kalubalen annobar COVID-19 da ambaliyar ruwa, kasar ta kuduri niyyar kammala ayyukata na yin adabo da talauci a bana.

Da yake bayyana nasarar da kasar ta samu a fannin yaki da talauci a matsayin mai muhimmanci, shugaba Xi ya bukaci dukkan bangarori su cimma burin da aka sa gaba kamar yadda aka tsara a mataki na karshe na aikin mai wahala. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China