2020-06-16 11:40:10 cri |
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da harin da 'yan ta'adda suka kai garuruwan Monguno da Nganzai na jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, harin da ya hallaka fararen hula da dama, tare da jikkata karin wasu mutanen, ya kuma lalata wasu kayayyakin gudanar da ayyukan jin kai a yankunan.
Cikin wata sanarwa da mataimakin kakakin sa Farhan Haq ya fitar a jiya Litinin, Mr. Guterres ya bayyana kaduwa da hare-haren, inda ya kuma gabatar da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su, da gwamnatin Najeriya, yana mai fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.
Jami'in ya kuma jaddada bukatar kare rayukan fararen hula, da jami'an ayyukan jin kai, kana da kare kayayyakin gudanar da ayyukan jin kai bisa tanajin dokokin kasa da kasa.
Daga nan sai ya jaddada goyon bayan MDD ga gwamnati da al'ummar Najeriya, a yakin da suke yi da ta'addanci, da masu tsattsauran ra'ayi.
Ana dai zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kaddamar da harin na ranar Asabar din karshen makon jiya. (Saminu)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China