Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mai dakin shugaban Zambiya ta yabawa tallafin da kamfanonin Sin ke baiwa kasar
2020-10-21 11:21:39        cri

Uwar gidan shugaban kasar Zambia, Esther Lungu, ta yabawa muhimmin taimakon da kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin ke cigaba da bayarwa wajen cigaban kasar Zambiyan.

A tsokacin da ta yi a lokacin karbar tallafin wasu kayayyaki daga kamfanin Higer Bus Zambia Limited, wani kamfanin kasar Sin, matar shugaban kasan ta ce, kasar Zambiya tana matukar farin ciki saboda taimakon da kamfanonin kasar Sin suke baiwa kasar.

Kayayyakin da kamfanin na Higer Bus Zambia Limited ya bayar sun hada da takunkumin rufe fuska 100,000 na yara.

Ta ce wannan gudunmawa za ta matukar taimakawa fannin koyar da ilmi a kasar, kana ta yabawa kyakkyawar dangantakar dake cigaba da kasancewa tsakanin Zambiya da Sin.

Wu Ming, babban manajan kamfanin Higer Bus Zambia Limited, ya ce an bayar da gudunmawar ne domin karfafa gwiwar yara 'yan makaranta marasa galihu.

Wu, ya yabawa kokarin da mai dakin shugaban kasar ta Zambiya ke bayarwa wajen ayyukan jin kai a kasar, ya kara da cewa, kamfanin ya amsa kiran da jakadan kasar Sin a Zambiya ya yi ne, inda ya bukaci kamfanonin dake aiki a kasar da su baiwa al'ummar Zambiya tallafi, domin sauke nauyin dake bisa wuyansu.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China