Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zambiya za ta kawar da dangogin cutar malariya nan da shekarar 2030
2019-10-30 11:11:21        cri
Gwamnatin kasar Zambiya ta tsara wani shirin hana duk wasu mace mace masu nasaba da cutar maleriya nan da shekarar 2030, wani babban jami'in gwamnatin kasar ya sanar da hakan a jiya Talata.

Ministan lafiyar kasar Chitalu Chilufya, ya ce shirin yana daga cikin manufofin da gwamnatin kasar ta tsara wanda ya shafi kara kaimi wajen kai daukin gaggawa don shawo kai da kuma kawar da cutuka a kasar.

Jami'in lafiyar ya bayyana hakan ne a lokacin yake tsokaci a gefen taron dandalin tattaunawar shirin kawar da cutuka na kasashe 8 wato (E8) na shiyyar kudancin Afrika (SADC) a birnin Gaborone, na kasar Botswana.

Shirin E8 na hadin gwiwa ne tsakanin kasashe 8 na kudancin Afrika inda zasu yi aiki tare a fadin kan iyakokin kasashen don kawar da cutar maleriya daga shiyyar nan da shekarar 2030. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China