Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Ghana sun fitar da tambarin tunawa da shekaru 60 da kafuwar hulda a tsakaninsu
2020-10-21 11:10:51        cri

Jami'ai a ofishin jakadancin kasar Sin dake Ghana tare da takwarorinsu na kasar Ghanan a ranar Talata, sun fitar da tambarin bikin murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A jawabin da ya gabatar a lokacin bikin, Zhu Jing, jami'in dake lura da ayyukan diflomasiyyar kasar Sin a Ghana, ya ce, gabatar da tambarin wata alama ce dake nuna kyakkyawar huldar diflomasiyya dake wanzuwa a tsakanin kasashen biyu.

A cewar mataimakain ministan sadarwa na kasar Ghana George Andah, kasar Ghana ta himmatu wajen kyautata alakarta da kasar Sin a yayin da kasashen biyu suke samun kyakkyawan sakamako don biyan bukatun kyautata rayuwar al'ummomin kasashen biyu da ayyukan gina muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a.

Shi dai wannan tambarin an tsara shi ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin kwararrun Ghana da na Sin, ta hanyar nuna wasu hotuna, ciki har da na muhimman ayyukan cigaba da aka gudanar a Ghana bisa tallafin kasar Sin.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China