Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ita ce ja gaba wajen girke kayayyakin soji a tekun kudancin Sin
2020-09-29 11:10:49        cri
A wani martani ga furucin ma'aikatar harkokin wajen Amurka dake cewa "Sin ta keta alkawarinta na girke kayayyakin soja a tsibiran Nansha", kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin, ya ce girke wasu kayayyakin tsaro na soji a tsibiran Nansha, na karkashin ikon kasar Sin.

Ya ce Amurka tana ta magana kan girke kayayyakin soji, amma a hakika, hanya take nema na karfafa girkewa da gudanar da ayyukan soji a tekun kudancin Sin da kuma ci gaba da babakere a yankin.

Wang Wenbin ya bayyana yayin wani taron manema labarai a jiya cewa, tsibirran Nanshan yanki ne na kasar Sin, kuma ayyukan gine-gine da kasar ke yi a yankinta, na da manufar biyan bukatun al'umma a yankin, domin kara samar musu da ma al'ummomin kasa da kasa, kayayyaki da hidimomi, da kuma sauke nauyin dake wuyanta. Ya ce a sa'i daya kuma, girke kayayyakin sojin na da nasaba da karewa da tsaron kai, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. Yana mai cewa, batu ne dake karkashin ikon kasar Sin da kuma doka.

Ya ce jiragen yakin Amurka sun yi ta gudanar da atisaye da ayyukan tattara bayanai akai akai a yankin, domin nuna iko da haifar da fargaba, yana mai cewa, Amurka ita ce ja gaba wajen girke sojoji a tekun kudancin Sin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China