Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministan lafiyar Afirka ta Kudu ya kamu da cutar COVID-19
2020-10-19 10:48:53        cri
Jiya Lahadi da dare, ministan harkokin kiwon lafiyar kasar Afirka ta Kudu Zweli Mkhize ya sanar da cewa, shi da uwargidansa sun kamu da cutar numfashi ta COVID-19.

Ya ce, a halin yanzu, suna killace kansu a gida, amma kuma, bai yi karin bayani kan yadda shi da uwargidansa suka kamu da cutar ba.

Ya ce, ya riga ya sanar da wadanda suka yi mu'amala da shi cikin 'yan kwanakin nan, domin su killace kansu, ciki har da iyalinsa da ma'aikatan ma'aikatar harkokin kiwon lafiya. A sa'i daya kuma, ya yi kira ga al'ummar kasar da su martaba ka'idojin hana yaduwar cutar numfashi ta COVID-19, su sanya abin rufe hanci da baki da kuma kaucewa shiga cunkoson jama'a, su kuma kula da lafiyarsu yadda ya kamata. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China