Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afirka ta Kudu ya yi magana a kan BLM
2020-09-23 10:25:30        cri

Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya yi magana a kan gwagwarmayar nan ta "Ran bakaken fata na da muhimmanci (BLM)", inda ya yi kira ga MDD, da ta yi kokarin kawar da wariyar launin fata.

Ramaphosa wanda ya bayyana haka, yayin jawabin da ya gabatar a babban taron MDD karo na 75, ya kuma bayyana cewa, za a tuna shekarar 2020 da muke ciki, da jerin gwanon da jama'a suka gudanar sassan duniya, game da batun nuna wariyar launin fata, karkashin laimar " Gwagwarmayar nan, ta ran babaken fata na da muhimmanci".

Ita dai wannan gwagwarmaya ta "BLM" ta samo asali ne a farkon wannan shekara, biyo bayan kashe wani bakar fata mai suna George Floyd, da wani jami'in dan sanda ya yi a Minneapolis na kasar Amurka.

Daga karshe Ramaphosa, ya yi kira da a kara daukar matakai, kan matsalar sauyin yanayi, da rage talauci da rashin daidaito, da kawar da amon bindigogi. Ya kuma yi kira da a yiwa kwamitin sulhu na MDD gyaran fuska, da samawa mata da 'yan mata abin dogara da kai.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China